H.K. Isra'ila Na Kokarin Kutsawa Cikin Afirka
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i7621-h.k._isra'ila_na_kokarin_kutsawa_cikin_afirka
Ziyarar Natanyaho A Kasar Kenya
(last modified 2018-08-22T06:58:32+00:00 )
Jul 04, 2016 07:50 UTC
  • H.K. Isra'ila Na Kokarin Kutsawa Cikin Afirka

Ziyarar Natanyaho A Kasar Kenya

An bayyana shirin ziyarar Pira ministan haramtacciyar Kasar Isra'ila zuwa kenya a matsayin kokarin kutsawa cikin nahiyar Afirka.

Jaridar Kasar Kenya ta "Star" ta buga a jiya lahadi cewa; Benjamin Natanyaho zai ciyarci Kenya domin bunkasa alakar kasuwanci da siyasa.

A yayin ziyarar Piraministan na haramtacciyar Kasar Isra'ila da kuma jami'an gwamnati Kenya za su rattaba hannu akan yarjeniyoyin da su ka shafi tsaro da noma.

Bugu da kari, za a kulla wata yarjejeniyar akan bude zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye daga Tel Aviv zuwa Nairobi.

Haramtacciyar Kasar Isra'ila dai tana kokarin samun goyon baya ne daga kasashen nahiyarta Afirka a fagen siyasar kasa da kasa.

Siyasar 'yan sahayoniya ta zaluntar palasdinawa da kuma shirnta na Nukiliya, na daga cikin dalilan da su ka hana kasashen Afirka da dama kulla alaka da ita.