Tashin Nakiya ya hallaka Mutane 8 a Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i7681-tashin_nakiya_ya_hallaka_mutane_8_a_somaliya
Mutane 8 sun rasu sanadiyar tashin Nakiya a kusa da birnin Magadushu na kasar Somaliya
(last modified 2018-08-22T11:28:33+00:00 )
Jul 05, 2016 14:38 UTC
  • Tashin Nakiya ya hallaka Mutane 8 a Somaliya

Mutane 8 sun rasu sanadiyar tashin Nakiya a kusa da birnin Magadushu na kasar Somaliya

Tashar telbijin din Press Tv dake watsa shirye-shiryenta daga nan birnin Tehran ta nakalto Abdulkadir Muhamad wani Jami'in 'yan sanda na kasar Somaliyan ya ce Nakiyar ta tashi ne a yayin ficewar wata karamar Bas dake dauke da fasinja a garin Lefouli mai nisan kilomita 18 daga kudu maso gabashin magadushu fadar milkin kasar

Baya ga Mutanan da suka mutu a kwai wasu da dama da suka samu munanar raunuka.

Rahotanni sun ce an karfafa matakan tsaro a yankin kudancin kasar bayan kai wannan mumunan hari ga fararen hular.

A daren Juma'ar da ta gabata ma wata Nakiya ta tashi da wata karamar Bas dake dauke da fajinsa a kusa da hanya garin Lafourde dake kudu maso yammacin Magadushu,lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula 20.

A baya bayan nan dai kungiyar ta'addancin nan ta Ashabab ta tsananta kai hare-hare kan fararen hula a kasar Somaliyan