Somaliya: An Kai Hari A Kasuwar Magadishu
Jul 06, 2016 06:19 UTC
Mutane 16 Sun Mutu A Wani Harin Da Aka Kai A Kasuwa.
Kamfanin dillancin Labarun Xinhua na kasar Sin ya nakalto daga birnin Magadishu cewa, a jiya talata a daidai lokacin da kasuwa ta cika da mutane, an kai hari da gurneti.
Mutanen da su ka jikkata sun kai 16.
Jami'in 'yan sanda Ahmad Abdul Afrah ya ce; Daga cikin wadanda su ka jikkatan da akwai wani sojan kasar, kuma tuni jami'an tsaro su ka bi sahun maharin.
Harin dai na jiya ya zo ne adaidai lokacin da mutane su ke cefanen karamar Sallah da ake yi a yau laraba.
Kawo ya zuwa yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin, sai dai an saba ganin irinsa daga kungiyar al-shabab.
Tags