Dauki Ba Dadi Tsakanin Direbobin Motar Haya Da 'Yan Sanda A Zimbabwe
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i7711-dauki_ba_dadi_tsakanin_direbobin_motar_haya_da_'yan_sanda_a_zimbabwe
Dauki ba dadi tsakanin direbobin motocin haya da 'yan sandan kwatar da tarzoma ya yi sanadiyyar jikkata mutane da dama a birnin Harare fadar mulkin kasar Zimbabwe.
(last modified 2018-08-22T06:58:33+00:00 )
Jul 06, 2016 05:06 UTC
  • Dauki Ba Dadi Tsakanin Direbobin Motar Haya Da 'Yan Sanda A Zimbabwe

Dauki ba dadi tsakanin direbobin motocin haya da 'yan sandan kwatar da tarzoma ya yi sanadiyyar jikkata mutane da dama a birnin Harare fadar mulkin kasar Zimbabwe.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya watsa rahoton cewa: Yan sanda kwantar da tarzoma sun farma direbobin motocin haya a birnin Harare fadar mulkin kasar Zimbabwe a lokacin da suke gudanar da zanga -zangar lumana a jiya Talata da nufin bayyana rashin amincewarsu da karin kudin tara da ake yi wa direbobin da suka saba dokokin haya lamarin da ya janyo gumurzu tsakanin bangarorin biyu.

Rahoton ya bayyana cewa: Yan sandan kwantar da tarzomar sun jikkata direbobi da dama ta hanyar amfani da karfi fiye da kima tare da kame wasu adadi masu yawa. Wannan tarzoma ta zo ne a daidai lokacin da malaman makarantun boko, likitoci da saurar ma'aikatan kiwon lafiya a kasar ta Zimbabwe ke gudanar da yajin aiki kan matsalar karancin kudin albashi.