Jami'an 'yan sandar Kenya sun dakile harin Ashabab
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i7750-jami'an_'yan_sandar_kenya_sun_dakile_harin_ashabab
Jami'an 'yan sandar dake yaki da ta'addanci a kasar Kenya sun sanar da Kashe wani dan kungiyar Ashabab tare da jikkata wani na daban.
(last modified 2018-08-22T06:58:33+00:00 )
Jul 07, 2016 01:23 UTC
  • Jami'an 'yan sandar Kenya sun dakile harin Ashabab

Jami'an 'yan sandar dake yaki da ta'addanci a kasar Kenya sun sanar da Kashe wani dan kungiyar Ashabab tare da jikkata wani na daban.

Kamfanin dillancin Labaran Xin Huwa na kasar China ya habarta cewa a jiya Laraba, Jami'an 'yan sanda masu yaki da ta'addanci a kasar Kenya sun hallaka wani Dan kungiyar Ashabab yayin musayar wuta a garin Kuwale

Baya ga haka, 'yan sandar na kenya sun sanar da jikkata wani Dan kungiyar Ashabab din na daban, inda suka ce suna kokarin kai wani harin bindiga ne, kuma a baya ma ana zarkin su da harin ta'addanci a kasar,

A Kwanakin baya ma Dakarun Sojin Kenyan sun sanar da kashe mayakan Ashabab 21 yayin wani gumurzu a kudancin Somaliya,inda a nasu bangare suka yi asarar Sojoji guda biyu, yayin da wasu biyar na daban suka jikkata.shidai wannan farmakin an kai shi ne a garin Afmadou mai nisan kilomita 50 daga gabashin iyakar kasar da Somaliya.

A baya bayan nan dai mayakan kungiyar ta Ashabab sun tsananta kai hare-hare kan jami'an tsaro, Jami'an Gwamnati , Dakarun kungiyar Tarayyar Afirka Amisson gami da fararen hula a kasar Somaliyan.