Najeriya: Hari A Masallaci A Najeriya
Jul 08, 2016 14:27 UTC
'Yan Kungiyar Bokoharam Sun Kashe Mutane Shida A wani harin kunar baki a masallaci.
Majiyar Sojan Najeriya ta ce; Wani dan kunar bakin wake ya kashe mutane 6 a cikin masallacin garin Dambua da ke jahar Borno.
Kakakin sojan Najeriya, Sani Usman, ya sanar a yau juma'a cewa; An dakile harin farko da aka so kai wa a babban masallaci garin, sai dai dan kunar bakin wake na biyu ya tashi kansa a cikin wani karamin masallaci.
Kawo ya zuwa an tabbatar da mutuwar mutane 6.
Babu wanda ya dauki alhakin kai harin, sai dai kungiyar bokoharam ce aka sani da hari irin wannan.
Tags