Tsagerun Niger Delta Sun Yi Barazanar Kashe Shugaban Kasar Nigeriya
Jagoran wata kungiya ta 'yan tsagerun yankin Niger Delta mai suna Niger Delta Avengers "NDA" a takaice ya yi barazanar halaka shugaban kasar Nigeriya Muhammadu Bukhari da dukkanin iyalan gidansa.
A wani fyaifyayin bidiyo da kungiyar tsagerun ta NDA ta fitar a ranar Alhamis da ta gabata: Jagoran kungiyar Ogenoghochuku ya yi barazanar kaddamar da nufin halaka shugaban Nigeriya Muhammadu Bukhari da iyalan gidansa matukar gwamnatin tarayyar Nigeriya ba ta hanzarta sakin madugun 'yan awaren yankin Biafra Nnamdi Kanu da take tsare da shi ba.
Jagoran kungiyar tsagerun Niger Deltan da ya fito da fuskarsa kwaro-kwaro ba tare da ya boye ba ya fayyace cewa: Kungiyar ta NDA ba an kafata ba ce a kan manufar kashe mutane amma ya zame dole ta dauki matakin aiwatar da kashe-kashen rayuka matukar ba a biya mata bukatu ba.