Wani Sabon Gumurzu Ya Kunno Kai Tsakanin Sojojin Gwamnatin Sudan Ta Kudu
Kakakin mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu James Gatdet Dak ya bayyana cewa: An yi wani musayar wuta mai tsanani tsakanin sojoji magoya bayan shugaban kasa Silva Kirr da na mataimakinsa Riek Machar a kusa da fadar shugabancin kasar da ke birnin Juba a jiya Juma'a.
Kakakin mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu James Gatdet Dak ya bayyanawa manema labarai cewa: Gumurzun ya kunno kai ne a lokacin da ake gudanar da zaman tattaunawa tsakanin shugaban kasa Silva Kirr da mataimakinsa a fadar shugabancin kasar da ke birnin Juba a jiya Juma'a dangane da musabbabin bullar rikici tsakanin magoya bayan bangarorin biyu a ranar Alhamis da ta gabata, inda ya zargi magoya bayan shugaban kasar da fara bude wuta kan sojoji magoya bayan Riek Machar.
Wata majiya ta bayyana cewa: Tuni dama an shirya zaman tattaunawan ne da nufin kame mataimakin shugaban kasar Riek Machar a lokacin da ya halacci zaman taron, sai dai kakakinsa James Gatdet Dak ya ce: Riek Machar din yana cikin koshin lafiya, kuma har yanzu babu cikakken bayani kan dalilin bullar musayar wutan.