Rikicin Baya bayan nan ya hallaka Mutane 115 a Sudan ta Kudu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i7849-rikicin_baya_bayan_nan_ya_hallaka_mutane_115_a_sudan_ta_kudu
Akalla Mutane 115 ne suka rasa rayukansu a rikicin baya bayan nan na kasar Sudan ta Kudu.
(last modified 2018-08-22T06:58:34+00:00 )
Jul 09, 2016 10:49 UTC
  • Rikicin Baya bayan nan ya hallaka Mutane 115 a Sudan ta Kudu

Akalla Mutane 115 ne suka rasa rayukansu a rikicin baya bayan nan na kasar Sudan ta Kudu.

Kamfanin dillancin Labaran Xin Huwa na Kasar China ya nakalto William Gatjiath kakakin 'yan adawa na kasar Sudan ta Kudu a wannan Assabar din na cewa a cikin Mutanan da suka rasa rayukansu sanadiyar rikicin ranar Juma'a a birnin Juba 35 Dakarun 'yan adawa ne, Sojoji 80 kuma na bangaren Gwamnati ne

Mista William ya ce a halin da ake dakin ajiyar gawawwaki na birnin Juba a ciki yake da gawawwaki na Dakarun kasar.

Rahoton ya ce An yi musayar wuta mai tsanani tsakanin sojoji magoya bayan shugaban kasa Silva Kirr da na mataimakinsa Riek Machar a kusa da fadar shugabancin kasar da ke birnin Juba a jiya Juma'a.

Kakakin mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu James Gatdet Dak ya bayyanawa manema labarai cewa: Gumurzun ya kunno kai ne a lokacin da ake gudanar da zaman tattaunawa tsakanin shugaban kasa Silva Kirr da mataimakinsa a fadar shugabancin kasar da ke birnin Juba a jiya Juma'a kuma jim kadan bayan fara musayar wutar , rikicin ya watsu a sauren yankunan kasar,

Wata majiya ta bayyana cewa: Tuni dama an shirya zaman tattaunawan ne da nufin kame mataimakin shugaban kasar Riek Machar a lokacin da ya halacci zaman taron, sai dai kakakinsa James Gatdet Dak ya ce: Riek Machar din yana cikin koshin lafiya, kuma har yanzu babu cikakken bayani kan dalilin bullar musayar wutan.