An gudanar da wani sabon garanbawul a hukumar DIA a Najeriya
Shugaba Buhari na Najeriya ya gudanar da wani sabon canji a hukumar ayyukan leken asiri ta fuskar ayyukan soji da tsaro a kasar.
A cikin wani sabon salo na yaki da kungiyar Boko Haram, Shugaban Najeriya Muhamad Buhari ya canza shugaban hukumar ayyukan leken asiri ta fuskar ayyukan soji da tsaro na kasar inda aka nada Air Vice Marshal Muhamadu Usman a matsayin sabon shugaban Hukumar, wanda ya maye gurbin Manja Janar Sardauna davies tsohon shugaban hukumar.
Kwararru da masu nazari kan harakokin tsaron kasar na ganin cewa wannan mataki da Shugaba Buhari ya dauka na a matsayin gudunar da gyara a harakokin gudanar da mulkin kasar inda a halin da ake ciki ya mayar da hankalin sa wajen tattara bayyanai sirri wajen tunkarar barazanar kungiyar Boko Haram a kasar.
A cewar Ministan harakokin tsaron kasar babban abin da gwamnatin Najeriya ke bukata na kawo karshen Boko Haram shi ne bayyanan sirri kan yadda kungiyar ke gudanar da ayyukanta na ta'addanci.
A cikin wani rahoton da kungiyar dake bin diddigin tashin hankali ta kasa da kasa ta watsa, Najeriya ita ce kasa ta hudu da aka fi samun asarar rayuka cikin shekarar 2015 da ta gabata bayan kasashen Siriya, Yemen da Iraki.