Najeriya : Masana Na Fargaban Fuskanci Yunwa A Arewa Maso Gabas
Jul 10, 2016 01:18 UTC
Tawagar masana dake sa ido akan rikicin da ake yi a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya ta nuna damuwa akan alamun fuskantar fari a yankin saboda ayyukan ta'adin ‘yan kungiyar Boko Haram a yankin.
Masanan sun fadi a wata sanarwa cewa mutane sama da miliyan uku na cikin wani hali a yankin kuma suna bukatar taimako gaggawa.
Kungiyoyi irin wannan kan ayyana za’a sami fari muddin suka lura cewa kashi 20% na yankin da ake zance na fama da matsalar rashin abinci, da rashin lafiya da sauran matsalolin rayuwa.
Dubban rayukan jama'a ne dai suka salwanta a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya sakamakon hare-haren na 'yan kungiyar Boko Haram.
Tags