Sharhin Bayan Labaru
Shugaban Kasar Zimbabwe Ya yi Suka Akan Ci gaba da kakabawa kasarsa Takunkumi.
Shugaba Robert Mugabe na kasar Zimbabwe, ya dora alhakin jinkirin biyan albashin ma'aikata a kasarsa, akan kasashen turai.!
Robert Mogabe wanda ya ke zantawa da 'yan jam'iyyarsa a arewa maso gabacin kasar, ya bayyana cewa; " Takunkumin da kasashen turai su ka kakabawa kasarsa, ya jefa kasar cikin matsaloli ta yadda ba za ta iya biyan albashin ma'aikatan gwamnati ba.
Mogabe ya kuma kara da cewa gwamnati tana namijin kokarin domin kawo karshen yajin aikin da likitoci da ma'aikatan jiyya da kuma malaman makarantu su ke yi.
Shugaban na kasar Zimbabwe ya kuma kirayi kasashen na turai da su dauke takunkumin da su ka kakabawa kasar tasa, kamar kuma yadda ya bukaci ma'aikatan gwamnatin kasar da su fahimci abinda ake ciki.
Tun a cikin shekarar 2000 ne dai Amurka da tarayyar turai su ka kakabawa kasar ta Zimbabwe takunkumai bisa zargin da su ka yi na magudin zabe da kuma take hakkin bil'adama.
Tare da cewa kasar ta Zimbabwe ta yi shekaru tana fuskantar takunkulin tattalin arziki, sai dai za a iya cewa a yanzu kura ta kai bango, saboda kasa biyan ma'aikata albashi.
A cikin kwanakin bayan nan ne dai wasu ma'aikatan gwamnatin kasar su ka tsunduma yajin aiki saboda rashin biyansu albashin watan yuni.
Su ma likitoci da malaman jiyya da malaman makaranta sun shiga yajin aiki akan batun na albashi.
Hatta sojoji da kuma jami'an tsaron kasar an jinkirita biyansu albashi na makwanni biyu, a watan da ya gabata.
Sauran ma'aikata kuwa sun sami dala 100 ne kadai daga cikin albashin nasu.
Gwamnatin kasar dai ta bayyana cewa kaso 80% na kasafin kufin kasar suna tafiya ne wajen biyan albashi. Ga shi kuwa kaso 90% na al'ummar kasar ba ma'aikata ba ne.
Su kuwa daliban makarantun kasar basu je maranta ba saboda yajin aikin da malamai su ke yi.
Suma matukan motocin haya a cikin kasar sun yi Zanga-zanga saboda yadda aka kara musu cin tara. An kuwa yi taho mu gama a tsakanin jami'an tsaro da kuma matuka motocin na taxi.
Babu wani lokaci a tarihin Zambabwe daga samun 'yancin kanta a 1980 zuwa yanzu, da al'ummar kasar su ka matsin lamba mai yawa sun tsuduma yajin aiki da kuma Zanga-zanga.
A watan da ya gabata ma mai mutanen garin Bolawayo su yi anga-zangar nuna kin jikin Robert Mogabe da mulkinsa. Sun kuwa bukaci shugaban na Zimbabwe da ya yi murabus.