Sarkin Kasar Morocco Ya Ki Ganawa Da Ministan Harkokin Wajen Saudiyya
Sarkin kasar Morocco Muhammadu na shida ya ki ganawa da ministan harkokin wajen kasar Saudiyya a ziyarar aikin da ya gudanar a kasar ta Morocco.
Ministan harkokin wajen kasar Saudiyya Adil Ajjubair ya mika kokensa ga fadar sarkin Saudiyya kan cewa a lokacin da ya ziyarci kasar Morocco, Sarkin kasar Muhammadu na Shida ya ki amincewa su gana lamarin da zai iya janyo gibi a alakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Wasu rahotonni suna bayyana cewa dalilin kin ganawar Sarki Muhammadu na Shida da ministan harkokin wajen kasar Saudiyya Adil Aljubairi ya samo asali ne sakamakon sabanin da ake da shi tsakanin kasashen Saudiyya da Morocco kan zaman taron shugabannin kasashen Larabawa karo na 76 da aka gudanar da a cikin watan Aprilun da ya gabata.