Yakin Basasa Ya Sake Kunno Kai A Kasar Sudan Ta Kudu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i7897-yakin_basasa_ya_sake_kunno_kai_a_kasar_sudan_ta_kudu
An ta jin harbe harbe a ko ina a birnin Juba babban birnin kasar Sudan ta Kudu
(last modified 2018-08-22T06:58:34+00:00 )
Jul 10, 2016 14:51 UTC
  • Yakin Basasa Ya Sake Kunno Kai A Kasar Sudan Ta Kudu

An ta jin harbe harbe a ko ina a birnin Juba babban birnin kasar Sudan ta Kudu

Dubban mutane ne a birnin Juba babban birnin kasar Sudan ta Kudu suke gudu suna barin birnin a yau Lahadi bayan fada ta kaure a sassa daban daban na birnin. Kamfanin dillancin labaran AFP ya ce fada ya barke tsakanin sojojin gwamnati da kuma na mayakan yan tawaye ne daga yammacin birnin inda dukkan bangarorin biyu suke da sansanonin sojojinsu.

AFP ya ce ana iya jin karar bindigogi a ko ina a cikin birnin a cikin tsawon ranar yau lahadi.

Shuwagabannin yankin wadanda suka hada da na Sudan da kuma Kenya sun yi kira ga bangarorin biyu da su dakatar da yaki, sun kuma kira taron gaggawa a gobe Litinin a birnin Adisababa na kasar Ethiopia don kashe wutan yakin. Har'ila yau komitin tsaro na majalisar dinkin duniya zai gudanar da wani taro a kebe don tattauna baton sabon yakin na Juba.

Bangarorin biyu dai suna zargin juna da sake tado fadar, amma ministan yada labarai na kasar ta Sudan ta kudu Michael Makuei ya ce har yanzun gwamnatin shugaba Silva Kiir ce take iko da birnin Juba babban birnin kasar.