Taron 'yan adawar kasar Gabon
'Yan adawa A kasar Gabon sun gudanar da wani taro domin yin alawadai da sake tsayawa takarar Shugaban kasar Ali Bango
Rahotanni daga Birnin Libreville sun ce dariruwan masu adawa da Shugaban kasar Gabon Ali Bagbo ne suka gudanar da wani zama jiya Lahadi a birnin Libreville domin bayyana adawar su da matsayin shugaban kasar na sake tsayawa takarar shugabacin kasar
A ranar Assabar din da ta gabata ce Shugaba Ali Bagbo ya mekawa Hukumar zaben kasar takardarsa na takarar shugabancin kasar.
A cewar 'yan adawar, da farko kamata ya yi shugaba Bango ya bayyace yanayin takardar aifuwarsa kafin ya meka takardar tsayawa takarar shugabancin kasar.
bisa sanarwar ta su, Shugaba Ali Bagbo bai iya tsayawa takarar shugabancin kasar saboda ba a aife shi a cikin kasar kamar yadda doka mai lamba ta 10 ta cikin kundin tsarin milkin kasar ta bayyana.