Masifar Yunwa Ta Fara Lashe Rayukan 'Yan Gudun Hijira A Arewacin Nigeriya
Kungiyoyin kare hakkin bil-Adama sun fara nuna damuwarsu kan bullar masifar yunwa da ta fara lashe rayukan 'yan gudun hijira a shiyar arewa maso gabashin tarayyar Nigeriya.
Shafin watsa labarai na Afrika Time ya watsa rahoton cewa: Masifar yunwa da karancin abinci mai gina jiki suna ci gaba da addabar 'yan gudun hijira da rikicin kungiyar Boko Haram ya tarwatsa ta hanyar raba su da muhallinsu, inda a halin yanzu haka masifar yunwa ta fara yin kamari a sansanonin 'yan gudun hijira daban daban da suke shiyar arewa maso gabashin kasar ta Nigeriya.
Rahoton ya bayyana cewa: A halin yanzu haka an fara samun bullar mutuwar kananan yara a sansanin 'yan gudun hijira da ke garin Banki na jihar Borno da ke kan iyaka da kasar Kamaru. Garin Banki yana daga cikin garuruwan da 'yan kungiyar Boko Haram suka kwace a lokacin da suke cin garuruwa da yaki, amma a halin yanzu garin yana karkashin ikon gwamnatin Nigeriya, kuma yana dauke da 'yan gudun hijira kimanin dubu ashirin kacal amma kayayyakin tallafi da ake raba wa 'yan gudun hijira ba su samun isa zuwa gare su.
A halin yanzu haka dai mafi yawan 'yan gudun hijira da suke yankuna daban daban na jihar Borno a shiyar arewa maso gabashin tarayyar Nigeriya suna rayuwa cikin aminci da zaman lafiya gwargwado sakamakon samun saukin hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram, amma kuma matsalar karancin abinci da kayayyakin kiwon lafiya da kuma tsabtar muhalli suna mummunar barazana ga rayuwarsu.
Tun daga lokacin da hare-haren kungiyar ta'addanci ta Boko Haram suka fara yin kamari a shekara ta 2009 zuwa yanzu, wasu alkaluma suna cewa; An samu hasarar rayukan mutane da suka haura 20, 000 tare da tilastawa wasu fiye da miliyan 2.3 barin muhallinsu, inda suka watsu a ciki da wajen kasar, kuma babban kalubale da 'yan gudun hijirar suke fuskanta a shiyar arewacin kasar ta Nigeriya shi ne; rashin abinci da kayayyakin kiwon lafiya.