Duban Mutane sun gudu daga birnin Juba na Sudan ta Kudu
A yayin da rikici tsakanin Sojojin Shugaba Salva keir na Sudan ta kudu da na mataimakinsa Riek Machar ke kara karami dubun dubutan fararen hula ne suka guda daga birnin Juba fadar milkin kasar S
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa daga birnin Juba ya habarta cewa dubun dubatan mazauna birnin Juba ne ke ci gaba da barin gidajensu sanadiyar rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa tsakanin Sojoji magoya bayan shugaban Kasar Salva keir da na mataimakinsa Riek Machar.
Ko wani bangaren na zarkin dan 'uwansa da fara kaimasa hari.
Rikicin ya ci gaba har a wannan Lahadi, inda alakaluma suka bayyana cewa adadin sojojin da suka mutu a tsakanin bangarorin biyu ya haura zuwa 270.
Wannan sabon rikici ya karya yarjejjeniyar sulhun da aka cimma tsakanin bangarorin biyu a shekarar bara.
Idan ba a manta ba rikicin cikin gidan na sudan ta kudun ya samo asali tun bayan da Shugaba Keir ya sauke mataimakinsa Riek machar daga kan mikaminka a shekarar 2013, bayan kokarin da kungiyoyin kasa da kasa, an samu nasarar cimma yarjejjeniyar sulhu a shekarar bara inda aka sake mayar da Riek Machar a kan mikaminsa, wanda hakan ya kawo karshen rikicin basasar da ya lakume rayukan mutane da dama.
A nasa bangare Babban saktaren MDD Ban Ki-Moon ya sake yin kira ga shugaban kasar ta Sudan ta Kudu da mataimakinsa da su yi kokarin dakatar da wannan rikici ba tare da bata lokaci ba.