Bokoharam Suna Samun Horo A Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i793-bokoharam_suna_samun_horo_a_somaliya
Shugaban Somaliya: "Yan Bokoharam suna samun horo ne a kasar Somaliya:
(last modified 2018-08-22T11:27:49+00:00 )
Feb 15, 2016 13:23 UTC
  • Bokoharam Suna Samun Horo A Somaliya

Shugaban Somaliya: "Yan Bokoharam suna samun horo ne a kasar Somaliya:

Shugaban Kasar Somaliya, ya bayyana cewa; 'yan kungiyar bokoharam suna samun horo ne a gabar ruwan kasar Somaliya kafin su koma gida.

Shugaban kasar Somaliyan Hasan Sheikh Muhamud wanda ya ke gabatar da jawabi a wurin tsaron karawa juna sani dangane da batun tsaro a kasar Jamus, ya kara da cewa; Kasar Somaliya tana fuskantar matsalolin fadace-fadace da cin hanci da rashawa da kuma hare-haren da alshabab ta ke kaiwa, sanann ya kara da cewa; Matukar ba a sami zaman lafiya ba, to baki dayan yankin zai fada cikin rikice-rikice.

Shugaban na kasar Somaliya ya kara da cewa; Da akwai kwararan dalilai da su ke tabbatar da cewa a wani lokaci a baya kungiyar bokoharam ta sami horo na soja a Somaliya sannan su ka koma gida Najeriya.