Sudan Ta Kudu : An Sake Gwabza Fada Da Muggan Makamai A Juba
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i7930-sudan_ta_kudu_an_sake_gwabza_fada_da_muggan_makamai_a_juba
Rahotannin daga Juba babban birnin kasar Sudan ta Kudu na cewa an sake gwabza mumunan fada a safiyar wannan Litinin.
(last modified 2018-08-22T06:58:34+00:00 )
Jul 11, 2016 08:05 UTC
  • Sudan Ta Kudu : An Sake Gwabza Fada Da Muggan Makamai A Juba

Rahotannin daga Juba babban birnin kasar Sudan ta Kudu na cewa an sake gwabza mumunan fada a safiyar wannan Litinin.

Shaidun gani da ido da majiyoyin diflomatsiya dama na kungiyoyi masu zamen kan su sun ce anyi ta barin wuta a wannan safiyar tsakanin bangarorin dake rikici da juna a birnin na Juba.

 

Kawo yanzu Allah kawai ya san adadin mutanen da suka rasa rayukan su a sabon rikicin daya barke tun a karshen makon jiya tsakanin dakarun dake biyaya ga shugaban kasar Salva Kiir da kuma na mataimakinsa Riek Mashar.

 

Saidai wasu rahotannin baya bayan nan sun ce adadin mutanen da suka mutu sanadin rikicin ya haura sama da 270, a yayin da dubban mutane ke tserewa daga birnin domin tsirada rayukan su.