Zaben Kasar Uganda
Feb 15, 2016 09:54 UTC
Tattaunawa Tsakanin 'Yan takarar Shugaban Kasar Uganda
'Yan takarar shugabancin Kasar Uganda sun gudanar da tattaunawa ta kai tsaye ta kafafen watsa labarun kasar.
Tattaunawar dai ta maida hankali ne akan batutuwan da su ka shafi siyasar waje ta kasar da kuma alaka da kasashen yamamcin turai. Har ila yau, an tambayi 'yan takarar da su bayyana matsayarsu dangane da aikewa da sojojin kasar zuwa kasashen yankin a karkashin dakarun tabbatar da zaman lafiya.
Baya ga shugaba Uweri Museveni da akwai 'yan takara bakwai da su ka kasance a tare da shi da su ka neman shugabancin kasar.
Za a gudanar da zaben shugaban kasar ta Uganda ne a ranar 18 ga watan Febrairu da ake ciki.
Tags