Sudan Ta Kudu : Kura Ta Lafa Bayan Tsagaita Wuta A Juba
Jul 12, 2016 06:47 UTC
Rahotanni daga Juba babban birnin kasar Sudan ta Kudu na cewa kura ta lafa a washe garin umurnin da jagororin bangarorin dake rikici a kasar sukayi na tsagaita wuta.
Masu aiko da rahotanni su ce a safiyar wannan Talata kura ta lafa ba a jiyo kara harbe harbe ba, babu wasu tankoki dake sintiri a birnin.
Hakazalika ma a kusa da filin sauka da tashin jiragen sama inda fada ya sake barkewa a Jiya kura ta lafa.
Tun dai ranar Juma'a data gabata ce fada ya barke tsakanin sojojin dake biyaya ga shugaba Salva Kiir da kuma wadanda ke biyaya ga mataimakinsa Riek Mashar lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 300 yayin da dubbai suka tsere daga birnin na Juba domin tsira da rayulansu.
Tags