Yajin Aiki Na Gama Gari Yayi Armashi A Kasar Guinea Conakry
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i808-yajin_aiki_na_gama_gari_yayi_armashi_a_kasar_guinea_conakry
Yajin aikin gama gari na sai baba ta gani da aka fara gudanarwa a kasar Guinea Conakry karkashin jagorancin kungiyoyin kwadago na kasar ya yi armashi sakamakon hadin kai da ma'aikata da al'ummar gari suka bayar.
(last modified 2018-08-22T06:57:49+00:00 )
Feb 15, 2016 14:05 UTC
  • Yajin Aiki Na Gama Gari Yayi Armashi A Kasar Guinea Conakry

Yajin aikin gama gari na sai baba ta gani da aka fara gudanarwa a kasar Guinea Conakry karkashin jagorancin kungiyoyin kwadago na kasar ya yi armashi sakamakon hadin kai da ma'aikata da al'ummar gari suka bayar.

A ganawarsa da manema labarai a birnin Conakry fadar mulkin kasar Guinea a yau Litinin; Babban sakataren gamayyar kungiyoyin kwadago na kasar ya bayyana cewar yajin aikin gama gari da suka kira a duk fadin Guinea Conakry ya samu karbuwa dari bisa dari domin harkokin rayuwa sun tsaya cak a babban birnin kasar Conakry da sauran manyan birane har da kanana.

Kungiyoyin kwadago a kasar ta Guinea Conakry sun fantsama cikin yajin aikin sai baba ta gani ne sakamakon kin amincewa da kiraye-kirayen da suka yi ga gwamnatin kasar kan rage farashin man fetur da kyautata rayuwar ma'aikata.

Rahotonni sun bayyana cewa; Gwamnatin Guinea Conakry ta girke jami'an tsaro a kan hanyoyi da makarantu musamman jami'o'i da ma'aikatun gwamnati a birnin Conakry fadar mulkin kasar domin tabbatar da doka da oda.