Amurka za ta tura Sojoji zuwa kasar Sudan ta Kudu
Cibiyar Rundunar Sojin Amurka dake yankin Afirka ta ce za ta kara tura Sojoji 40 domin taimakawa fararen hula ficewa daga birnin Juba
A wata sanarwa da ya fitar a wannan Laraba, Kakakin Rundunar Sojin Amurka dake yankin Afirka jennifer Dyrkz ya ce sun dauki wannan mataki domin kare 'yan kasar su dake zaune a kasar Sudan ta kudu.
A tana bangare, Ma'aikatar harakokin wajen Amurka dake birnin Juba ta ce ta tanadi jiragen sama da za su kwashe 'yan kasar daga cikin kasar ta kudun.
An kwashe kwanaki biyar ana gobza fada tsakanin Sojojin dake biyayya da Shugaban kasar Salva Keir da kuma na mataimakinsa na farko Riek Machar, lamarin da ya yi sanadiyar lashe rayukan Mutane kimanin 300.
Har ila yau rikicin ya sanya an dakatar da tashi ko sauka na dukkanin Jiragen zirga-zirgen fasinja a kasar, a halin da ake ciki Jirgen kai agajin gaggauwa ne kawai ke zirga-zirgar kai agaji tare da kwashe 'yan kasashen waje daga birnin Juba.
Kasar Jamus ita ma ta sanar da kwashe 'yan kasar ta da ma wasu 'yan kasashen waje daga birnin na Juba.
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa kimanin fararen hula dubu 36 ne suka gudu suka bar gidajensu daga birnin Juba sanadiyar musayar wuta na kwanaki biyar din tsakanin Sojojin dake biyayya da Shugaban kasar Salva Keir da kuma na mataimakinsa na farko Riek Machar.
A nasa bangare Shugaban Kasar Sudan ta Kudu ya sanar da yin afuwa ga Dakarun dake biyayya ga mataimakin Shugaban kasar na farko Riek Machar