Gunea Conakry:
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8092-gunea_conakry
Yaran Kasar Gunea Conakry Ba su Samun Abinci Mai Gina Jiki
(last modified 2018-08-22T06:58:35+00:00 )
Jul 14, 2016 01:59 UTC
  • Gunea Conakry:

Yaran Kasar Gunea Conakry Ba su Samun Abinci Mai Gina Jiki

Gwamnatin Kasar Gunea ta sanar da cewa; kaso 1%3 na yaran kasar ba su samun abinci mai gina jiki.

Kamfanin dillancin labarun Xinhua, daga birnin Conakry ya ce: " Ma'aikatar kiwon lafiyar kasar ta Gunea da ta fitar da wani bayani ta ce, da akwai yaran da adadinsu ya haura dubu dari biyar da basu samun abinci mai gina jiki, da hakan ya ke a matsayin wani babban kalubale ga kasar."

Har ila yau, rahoton ya ambato kwararrun kiwon lafiya na kasar na cewa; hanyar magance matsalar ita ce ta inganta abincin iyaye mata a lokacin da su ke da juna biyu. Haka nan kuma baiwa jarirai nono zalla na tsawon watanni shida bayan haihuwarsu da kuma yi musu alluran rigakafi.