Sudan Ta Kudu
Shugaban Kasar Sudan Ta Kudu ya yi Afuwa Ga 'Yan tawaye
Shugaban Kasar Sudan Ta Kudu Ya yi afuwa ga 'yan tawayen da su ka kai wa babban birnin kasar hari.
Majiyar Gidan Radiyo da Telbijin ta Iran daga birnin Juba, ta ambato cewa; tun a ranar talatar da ta gabata ne dai Shugaban Sudan ta Kudu, Silva Kir ya yi alkawalin yin afuwar ga 'yan tawayen da su ka kai hari a babban birnin kasar.
Fadan da aka yi a tsakanin magoya bayan Silva Kir da mataimakinsa Reik Machar, ya ci rayukan mutane fiye da 300.
A gefe daya, majiyar hukumar 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya, ta ce; dubban mutanen kasar ne su ka tsallaka iyaka zuwa garin Kakuma da ke arewa maso yammacin kasar Kenya domin samun mafaka.