Sudan ta Kudu : Sojojin Uganda Sun Shiga Juba
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8110-sudan_ta_kudu_sojojin_uganda_sun_shiga_juba
Wani ayarin motocin sojojin Uganda ya shiga Sudan ta Kudu a wannan Alhamis da nufin kwashe 'yan kasar ta Uganda da suka makalle a Juba.
(last modified 2018-08-22T06:58:35+00:00 )
Jul 14, 2016 07:27 UTC
  • Sudan ta Kudu : Sojojin Uganda Sun Shiga Juba

Wani ayarin motocin sojojin Uganda ya shiga Sudan ta Kudu a wannan Alhamis da nufin kwashe 'yan kasar ta Uganda da suka makalle a Juba.

kanfanin dilancin labaren AFP ya ce ayarin motocin dauke da makamai sun kusa kai cikin kasar Sudan ta Kudun domin kwashe 'yan kasarsu kimanin 3.000 a birnin na Juba inda aka kwashe kwanaki ana gwabza fada tsakanin dakarun dake biyaya ga shugaba Salva Kiir da kuma na mataimakinsa Riek Mashar.

A haklin da ake ciki dai mataimakin shugaban kasar kana jagoran ‘yan tawaye ya fice da dakarunsa daga Juba, yayin da aka shiga kwana na uku na tsagaita wuta tsakaninsu da dakarun gwamnati.

An dai kwashe kwanaki biyar ana gobza fada tsakanin bangarorin biyu lamarin da ya yi sanadiyar hasara rayukan mutane kimanin 300, tare da tilastawa dubbai tserewa daga birnin domin tsira da rayukansu.