Kwararen 'yan gudun hijrar Sudan ta kudu zuwa kasashe Makobta
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8137-kwararen_'yan_gudun_hijrar_sudan_ta_kudu_zuwa_kasashe_makobta
Rikicin baya bayan nan na kasar Sudan ta kudu ya yi sanadiyar ficewar duban 'yan kasar zuwa kasashe makobta
(last modified 2018-08-22T06:58:36+00:00 )
Jul 15, 2016 00:08 UTC
  • Kwararen 'yan gudun hijrar Sudan ta kudu zuwa kasashe Makobta

Rikicin baya bayan nan na kasar Sudan ta kudu ya yi sanadiyar ficewar duban 'yan kasar zuwa kasashe makobta

A halin da ake ciki, Kasar Sudan na dauke da bakuncin 'yan sudan ta kudu kimanin dubu 500,daga watan Maris din wannan shekara, Gwamnatin Sudan ta dauki kudirin cewa za ta yi mu'amala tare da 'yan kasar Sudan ta Kudu kamar sauren 'yan kasashen waje,inda ta bukace su da amfani da Pasport.

Mista Herve Ladsous Shugaban Dakarun tsaro da Sulhu na MDD dake kasar Sudan ya bayyana damuwarsa kan sake billar sabon rikici a kasar Sudan ta Kudu.

A yayin da yake meka rahoto a gaban Kwamitin tsaro na MDD, Mista Herve Ladsous ya bukaci taimakon gaggawa daga kasashen yankin gabashin Afirka a kan su tura Dakarunsu birnin Juba da akalla za su taimaka wajen tabbatar da tsaro a filin sauka da tashi na birnin, wanda hakan zai sanya a samu damar fitar da 'yan kasashen waje daga cikin kasar.

A ranar 7 ga wannan wata da muke cikin ne wani sabon rikici ya barke tsakanin Sojoji masu biyayya ga shugaban kasar Sudan ta Kudun Salva Keir da kuma na mataimakinsa Riek Machar, Alkaluma sun bayyana cewa akalla Mutane 300 ne suka rasa rayukansu a gumurzun da aka kwashe kwanaki biyar ana yinsa.

A cewar Mista Herve Ladsous, adadin Mutanan da suka rasa rayukansu ya haura 300 idan aka yi la'akari da yadda mazauna birnin Juban ke gudu domin tsira da rayukansu.

Rahoton karshe da aka bayar na adadin 'yan gudun hijra na kasar sudan ta kudun yahaura zuwa dubu 42 sanadiyar rikicin baya bayan nan, kuma aksarinsu sun gudu ne zuwa kasashen Sudan da Kenya.

Babban Kwamishina mai kula da 'yan gudun hijra na MDD ya bukaci kasashen dake makobtaka da kasar, su buda iyakokinsu ga fararen hula domin samun mafuka.

Kafin wannan rikicin, sansanin 'yan gudun hijra na Kakuma dake arewa maso yammacin Kenya na dauke da 'yan gudun hijrar Sudan ta kudu kimanin dubu dari. A kasar Sudan, Dakarun tsaro da Sulhu na MDD sun tabbatar da cewa a halin da ake cikin sun karbi 'yan gudun hijrar birnin Juba kimanin Dubu bakwai.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta sanar da cewa a halin da ake ciki, a kwai Mutane kimanin dubu 36 da suka nemi mafuka a Makarantu da kuma coci coci dake birnin Juba saidai suna fama da matsalar tsabtaceccen ruwa sha da kuma guraren tsarkake jiki.

Mista Ladsous ya ce duk da cewa Sojojin Shugaban Keir suke rike da Birnin Juba, to amma a kwai yuyuwar sake barkewar rikicin saboda Sojojin dake biyayya da mataimakin shugaban kasar na farko wato Riek Mashar na jibke a gariruwan dake kewayen birnin na Juba kamar su Malakal,Nil Aliya da Leer.

Riek Machar ya bukaci MDD da ta sanya shamaki a tsakanin yankunan da Sojojin sa suke da kuma na Shugaban kasa.

A nasa Bangare Shugaban kasar Salva Keir ya sanar da yin afuwa ga Sojojin da suka yaki Sojojin dake biyayya da shi.

Shugaban kasar Amurka Barak Obama ya bada izini tura Sojojin Amurka kimanin 47 domin kare 'yan kasar sa dake birnin na Juba, ita kuma Kungiyar bunkasa tattalin arziki ta gabashin Afirka wato IGAD ta bukaci da a kara yawan Dakarun tsaro da sulhu sannan kuma a kara musu kayan aiki na zamani a kasar Sudan ta Kudun.