Kungiyar Kasashen Larabawa Na Shirin Bunkasa Alaka Da Sudan Ta Kudu
Babban sakataren kungiyar kasashen larabawa Ahmad Abul Ghaith ya bayyana cewa kungiyar tana da zimmar kara bunkasa alakarta da kasar Sudan ta kudu.
Ahmad Abul Ghaith ya bayyana hakan ne a yammacin jiya a lokacin da yake ganawa da shugaban kasar Sudan Umar hassan Albashira birnin khartum, inda ya sheda cewa; a cikin shekara ta 2011 Sudan ta kudu ta kasance a cikin kasashen larabawa, domin a lokacin tana cikin jamhuriyar Sudan, kuma har yanzu harshen larabci shi ne shi ne harshen da ya hada dukkanin al'ummomin kasar.
Abul Ghaith ya kara da cewa a zaman taron ministocin harkokin wajen kasashen larabawa da za a gudanar nan gaba zai gabatar da wanann bukata, domin amincewa da Sudan ta kudu a matsayin mamba mai sanya ido a kungiyar kasashen larabawa.