Guinea : 'Yan Adaza Zasu shiga Zanga-zanga
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8155-guinea_'yan_adaza_zasu_shiga_zanga_zanga
'Yan adawa a kasar Guinea sun sanar da shirin shiga zanga-zanga a duk fadin kasar daga ranar 4 ga watan gobe domin nuna rashin jin dadin su akan rashin iya tafiyar da mulki na mahukuntan kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:36+00:00 )
Jul 15, 2016 04:46 UTC
  • Guinea : 'Yan Adaza Zasu shiga Zanga-zanga

'Yan adawa a kasar Guinea sun sanar da shirin shiga zanga-zanga a duk fadin kasar daga ranar 4 ga watan gobe domin nuna rashin jin dadin su akan rashin iya tafiyar da mulki na mahukuntan kasar.

'Yan adawan dai sun ce zasu fara zanga-zangar a Conakry babban birnin kasar domin kalubalentar salon mulkin Alpha Conde wanda suka danganta da rashin iya siyasa da kuma tabarbarewar tattalin arzikin kasar.

Hakazalika 'yan adawa sun ce gwamnatin kasar da sabawa yarjejebiyar da aka cimma a yayin tattaunawar data gabata.

Daga cikin dai bukatar 'yan adawa har ganin an hukunta duk wani hannu a muzgunawar da aka yi wa masu zanga-zanga a wacen lokacin, da kuma batun jadawalin zaben kananen hukumomi.