Sudan Ta Kudu : An Fara Samun Natsuwa A Juba
Rahotannin daga Sudan ta Kudu na cewa, an fara samun kwanciyar hankali a birnin Juba, kuma ba a sake samun abkuwar wata matsala a fannin tsaro ba kawo yanzu.
A nasu bangaren, manyan kusoshin kasashen Afirka dake halartar taron kolin kungiyar tarayyar Afirka AU a Kigali na kasar Ruwanda, sun nuna damuwa kan yanayin da ake ciki a Sudan ta Kudu, tare da fatan ganin bangarorin kasar da ba sa ga maciji da juna zasu kawo karshen halin ja-in-ja da suke yi, da kiyaye yanayin tsagaita bude wuta, don maido da kwanciyar hanakali a kasar.
Ban da haka kuma, masu halarta taron sun nuna yabo ga ma'aikatan wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu.
An dai kwashe kwanaki biyar ana gobza fada tsakanin bangarorin biyu lamarin da ya yi sanadiyar hasara rayukan mutane kimanin 300, tare da tilastawa dubbai tserewa daga birnin domin tsira da rayukansu.