Chadi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8212-chadi
Kasar Chadi ta yi gargadi akan yaduwar Bokoharam.
(last modified 2018-08-22T06:58:36+00:00 )
Jul 16, 2016 14:20 UTC
  • Chadi

Kasar Chadi ta yi gargadi akan yaduwar Bokoharam.

Shugaban hukumar da ta ke fada da ayyukan ta'addanci a kasar Chadi ya yi gargadi akan yiyuwar yaduwar hare-haren ta'addanci na kungiyar bokoharam.

shugaban hukumar fada da ayyukan ta'addancin na Chadi, Rvmyr Convade, ya fada a yau asabar cewa; Kungiyar ta Bokoharam tana da matukar hatsari a nahiyar Afirka, kuma matukar shugabannin na Afirka ba su yi tunanin da ya dace ba, to sakamakon da zai biyo baya yana da hatsarin gaske.

Bugu da kari, Convade ya ce; Tare da cewa a cikin watannin bayan nan an raunana kungiyar saboda munanan hare-haren da aka kai mata, amma duk da haka yanayin yana da hatsarin gaske.

Rikicin bokoharam dai ya tarwatsa mutanen da su ka kai miliyan biyu da maida su 'yan gudun hijira a cikin gida da kuma kasashen makwabta.