Cote De Voire
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8215-cote_de_voire
Majalisar Dinkin Duniya Na Son Ganin Komawar 'yan gudun hijirar Cote De Voire Gida
(last modified 2018-08-22T06:58:36+00:00 )
Jul 16, 2016 14:24 UTC
  • Cote De Voire

Majalisar Dinkin Duniya Na Son Ganin Komawar 'yan gudun hijirar Cote De Voire Gida

Hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya, ta bayyana fatanta na ganin 'yan gudun hijirar Cote De Voire sun koma gida cikin gaggawa.

Cibiyar Watsa Labaru ta "African Time" ta buga cewa; Gwamnatin kasar ta Cote De Voire da kuma wakilan hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya sun bude wata tattaunawa ta kwanaki 3 akan yadda za a mayar da 'yan gudun hijirar kasar da su ke a kasashen makwabta, zuwa gida.

A yayin taron dai, hukumar 'yan gudun hijirar ta majalisar dinkin duniya ta ce, za ta bai wa gwamnatin kasar COte De Voire hadin kai domin komawar 'yan gudun hijirar zuwa gida da gaggawa.

Rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa na 2010 ne ya sa 'yan kasar da dama su ka tsallaka iyaka zuwa kasashen makwabta da su ka hada Liberia,Togo da Ghana.