Kiran Kungiyar Tarayyar Afirka Ga Kasar Sudan Ta Kudu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8218-kiran_kungiyar_tarayyar_afirka_ga_kasar_sudan_ta_kudu
Tarayyar Afirka Ta Bukaci Masu Fada Da Juna A Sudan Ta Kudu Da Su yi Aiki Da Tsagaita Wuta.
(last modified 2018-08-22T06:58:36+00:00 )
Jul 16, 2016 14:29 UTC
  • Kiran Kungiyar Tarayyar Afirka Ga Kasar Sudan Ta Kudu

Tarayyar Afirka Ta Bukaci Masu Fada Da Juna A Sudan Ta Kudu Da Su yi Aiki Da Tsagaita Wuta.

Kamfanin Dillancin Labarun Xinhua na kasar Sin ya nakalto majiyar kungiyar tarayyar Afirka da ke taro a kasar Rwanda na yin kira ga shugaba Silva Kiir da mataimakinsa Reikh Machar da su yi aiki da tsagaita wutar yaki.

Ministar harkokin Wajen Rwanda Louise Mushikiwabo ta bayyana cewa; kungiyar tarayyar afirka tana bin diddigin abinda ya ke faruwa a cikin kasar Sudan ta kudu daga kusa, kuma mambobin kungiyar za su yi iya kokarinsu domin bada kariya ga fararen hula.

A halin da ake ciki a yanzu dai kungiyar ta Afirka tana nuna cikakken goyon bayanta ga shugaba Silva Kiir da kuma mataimakinsa Reikh Machar, don haka su ke kira a gare su da su ci gaba da tabbatar da zaman lafiya.

Kwakani kusan 10 kenan da aka fara fada a tsakanin masu goyon bayan shugaban kasar Sudan ta kudu, da kuma mataimakinsa a birnin Juba. Daruruwan mutane ne dai su ka rasa, rayukansu, yayin da wasu kuma su ka jikkata.