Goyon Bayan 'Yan Adawan Zimbabwe Ga Yunkurin Kungiyoyin Fararen Hulan Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8224-goyon_bayan_'yan_adawan_zimbabwe_ga_yunkurin_kungiyoyin_fararen_hulan_kasar
Shahararren dan adawar siyasar Zimbabwe Morgan Tsvangirai ya nuna goyon bayansa ga yunkurin kungiyoyin fararen hulan kasar a fagen nuna adawa ga siyasar jam'iyya mai mulki a kasar ta ZANU-PF karkashin shugabancin Robbert Mugabe.
(last modified 2018-08-22T06:58:36+00:00 )
Jul 17, 2016 01:15 UTC
  • Goyon Bayan 'Yan Adawan Zimbabwe Ga Yunkurin Kungiyoyin Fararen Hulan Kasar

Shahararren dan adawar siyasar Zimbabwe Morgan Tsvangirai ya nuna goyon bayansa ga yunkurin kungiyoyin fararen hulan kasar a fagen nuna adawa ga siyasar jam'iyya mai mulki a kasar ta ZANU-PF karkashin shugabancin Robbert Mugabe.

Shugaban jam'iyyar MDC Morgan Tsvangirai da ya shafe tsawon shekaru yana jagorantar gungun 'yan adawa a Zimbabwe tare da gwagwarmayar ganin ya kawo karshen shugabancin Robbert Mugabe a kasar amma hakan ya cutura, a halin yanzu dama ta samu gare shi ta hada kai da gamayyar kungiyoyin fararen hula karkashin jagoranci Pastor Mawarira wajen ganin ya cimma manufarsa.

Yunkurin baya -bayan nan na kungiyoyin fararen hula da na kwadago karkashin jagorancin Pastor Mawarira a kasar Zimbabwe musamman gudanar da yajin aikin gama gari a duk fadin kasar da nufin nuna adawa ga siyasar gwamnatin Robbert Mugabe ta murkushe fararen hula da suke adawa da manufofin gwamnatin kasar musamman matakin baya-bayan nan da jami'an tsaro suka dauka a birnin Harare na yin amfani da karfi fiye da kima kan fararen hula ta samu cikakken goyon baya daga Jagoran 'yan adawan kasar Morgan Tsvangirai duk da cewa baya da hannu a shirya yajin aikin na gama gari.

Manazarta harkokin siyasa da masu fashin baki suna bayyana cewa; Matakin da kungiyoyin fararen hula da na kwadago suka dauka na bayyana adawarsu ga siyasar gwamnatin Zimbabwe lamari ne da zai kara karfi ga 'yan adawar siyasar kasar tare da karfafa Morgan Tsvangarai kan manufar siyasarsa ta nuna adawa da gwamnatin Robbert Mugabe.

A makon da ya gabata ne Pastor Mawarira ya jagoranci wani gagarumin yajin aiki a duk fadin kasar Zimbabwe inda yajin aikin ya hada da kauracewa ma'aikatun gwamnati, makarantu, rufe shagunan kasuwanci, dakatar da zirga-zirgar ababan hawa da zirga-zirgan jama'a a sassa daban daban na kasar lamarin da ya girgiza mahukuntan Zimbabwe, kuma masharhanta ke ganinsa a matsayin bullar wani sabon yunkurin adawa ne ga gwamnatin Mugabe.

Robbert Mugabe dan shekaru 92 a duniya ya fara jagorancin kasar Zimbabwe ne a matsayin fira minista tun a shekara ta 1980 zuwa 1987, sannan ya zame farkon shugaban kasa mai cikakken iko a shekara ta 1987 kuma har zuwa yanzu shi ke shugabantar kasar, kuma wata majiya ta kusa da shi na cewa Mugabe yana hankoron sake tsayawa a zaben shugabancin kasar ta Zimbabwe a shekara ta 2018, duk da cewa wasu rahotonni na nuni da cewa Mugabe yana fama da matsalar rashin lafiya sakamakon yawan shekaru amma dai ana boyewa.

A halin yanzu haka dai a fagen siyasar Zimbabwe ana zaton a tsakanin mataimakin shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa da matar shugaban kasar Grace Mugabe ne za a samu wanda zai maye gurbin Robbert Mugabe a bayan mutuwarsa, yayin da a gefe guda kuma masu fashin baki ke ganin Pastor Mawarira zai maye gurbin madugun 'yan adawar kasar musamman ganin yadda tauraronsa yake haskakawa a halin yanzu haka.