Shugaba Albashir na kasar Sudan zai halarci taron Kungiyar AU a Ruwanda
(last modified Sun, 17 Jul 2016 06:13:53 GMT )
Jul 17, 2016 06:13 UTC
  • Shugaba Albashir na kasar Sudan zai halarci taron Kungiyar AU a Ruwanda

Shugaban Kasar Sudan Umar Albashir ya ce zai halarci taron Kungiyar Tarayyar Afirka da zai gudana a kasar Ruwanda duk kuwa da cewa a kwai sammacin kotun hukunta manyan laifuka ta Duniya a kansa

Jaridar New York Times ta nakalto Ministan Harakokin wajen Ruwanda na cewa matukar dai Shugaba Albashir din ya Halarci taron Kungiyar AU a Kigali, kasar sa ba za ta meka shi ga kotun hukunta manyan laifuka ta Duniya ba.

A yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai, Ministan ya tabbatar da cewa Kasar sa ta samu wasikar Kotun hukunta manyan Laifuka ta Duniya, inda ta bukaci cewa da zarar Shugaba Albashir ya sanya kafarsa a birnin Kigali, a kame shi kuma a meka mata shi, saidai kasar sa ba zata bi umarnin kotun ba.

Kotun hukunta manyan laifukan ta Duniya na zarkin Shugaba Albashir da laifin kisan killa ga Al'ummar yankin Darfur.

Duk da sammacin na kotun, Shugaba Albashir ya ziyarci kasashen Afirka da dama, a watan Mayun da ya gabata ma ya halarci bikin rantsar da Shugaban kasar Ruwanda.