An yi gargadin rasa rayuka a Sudan ta kudu.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8239-an_yi_gargadin_rasa_rayuka_a_sudan_ta_kudu.
Hukumar samar da abinci da ayyukan Noma ta MDD FAO ta yi gargadin karuwar assarar rayuka a kasar Sudan ta kudu.
(last modified 2018-08-22T06:58:36+00:00 )
Jul 17, 2016 01:45 UTC
  • An yi gargadin rasa rayuka a Sudan ta kudu.

Hukumar samar da abinci da ayyukan Noma ta MDD FAO ta yi gargadin karuwar assarar rayuka a kasar Sudan ta kudu.

A wani Rahoto da ta fitar a wannan Assabar, Hukumar samar da abinci da ayyukan Noma ta MDD FAO,ta ce matukar aka ci gaba da tashin hankali a kasar Sudan ta kudu, za a fuskanci masifar asarar rayukan mutane da dama sanadiyar rashin abinci.

Hukumar ta kara da cewa a halin da ake ciki milyoyin Jama'a ne ke fuskantar barazanar karancin abinci a kasar, matukar ba a kawo karshen rikicin ba, shakka babu Mutane da dama ne za su rasa rayukansu sanadiyar rashin abinci.

Har ila yau hukumar ta bukaci Kunigiyoyin kasa da kasa da su gaggauta kai agaji zuwa kasar Sudan ta Kudu.

A makon da ya gabata ma Evin Aso babban jami'i a MDD ya bayyana damuwar sa kan halin da Fararen hula ke ciki a yankunan da yaki ya daidaita a Sudan ta Kudun.

An bayyana cewa yakin cikin gidan ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da raba duban Mutane da gidajensu a yankunan arewa maso yammacin kasar.