Gabon : 'Yan Takara 14 Ke Zawarcin Kujera Shugaban Kasa
Hukumar zabe a Gabon ta amunce da sunayen mutane 14 a zaben shugaban kasar na ranar 27 ga watan Agust mai zuwa.
Daga cikin masu neman takara 19 da suka ajiye takardun su kotun ta amunce da takara mutane 14 tare da yin watsi da takara mutane biyar saboda rashin cikar takardunsu..
A yanzu dai 'yan takara 14 ne ciki har da shugaba mai ci Ali Bongo Ondimba zasu fafata a zaben.
Mr Bongo dan shekara 57 zai kuma fafata da wasu jiga-jigan 'yan adawa da suka hada da tsohon shugaban kwamitin kungiyar tarayya Afrika Jean Ping da kuma tsohon shugaban majalisar dokokin kasar Guy Nzouba Ndama da kuma tsohon gwamnan babban bankin afrika ta tsakiya Casimir Oye Mba.
'yan adawa dai a wannan kasa sun jima suna korafi akan takara Ali Bongo wanda suka ce dan asalin kasar Najeriya ne wanda dan riko ne ga tsohon shugaban kasar Omar Bongo, wanda kuma takarasa ta sabawa kundin tsarin mulkin kasar.
Yanzu dai 'yan adawa nada kwanaki uku domin kalubalantar takara Ali Bongo a gaban kotun tsarin mulkin kasar.