An Bude Taron Kolin (AU) A Kigali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8257-an_bude_taron_kolin_(au)_a_kigali
A wannan Lahadi shugabannin kasashe mambobin Kungiyar Tarayyar Afirka suka fara taro kolin kungiyar a karo na 27 a Kigali babban birnin kasar Rwanda.
(last modified 2018-08-22T06:58:36+00:00 )
Jul 17, 2016 11:55 UTC
  • An Bude Taron Kolin (AU) A Kigali

A wannan Lahadi shugabannin kasashe mambobin Kungiyar Tarayyar Afirka suka fara taro kolin kungiyar a karo na 27 a Kigali babban birnin kasar Rwanda.

A Daura da taron shugabanin sun tattauna akan halin da ake ciki a Sudan ta Kudu, da bukatar kasar Marocco na dawowa cikin kungiyar bayan shekaru 30 da ficewa daga cikin kungiyar, da kuma batun wanda zai gaji Mme Nkosazana Dlamini-Zuma a shugabancin kungiyar.

'ya takara uku ne ke zawarcin kujerar da suka hada da ministocin harkokin wajen Botswana da na Equatorial Guinea da kuma mataimakiyar shugaban kasar uganda.

Saidai rahotanni sun ce mai yiwa a jinkirta zaben har zuwa taro na gaba a Adis Ababa saboda rashin tantancar masu takara.

Daga cikin muhimman batutuwan da taron zai mayar da hankali akwai dangantakar kasashen da Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ke Hague da kuma shirin kungiyar na yin Fasfo na bai-daya.