Sabon Passport Na Tarayyar Afirka
Sabon Passport Na Tarayyar Afirka
Jim kadan bayan bude taron kungiyar tarayyar Afirka, an raba sabon passport na tarayyar Afirka ga wasu shugabannin kasashe.
Kamfanin Dillancin Labarun (AFP) ya ce; wadanda aka bai wa sabon takardar izinin shiga da fice din ta Passport, sune shugaban kasar Rwanda Paul Kigame, da shugaban kasar Chadi Idris Deby.
Shugabar Tarayyar Afirka, Dlamini Zuma Nkosazana ta bayyana Sabon Passport din da cewa; Abin alfahari ne a ce dan Afirka zai yi zirga-zirga ko'ina a cikin nahiyar cikin 'yanci."
Bugu da kari, Zuma, ta ce; Dukkanin kasashe mambobi sun yi alkawalin samar da yanayin da ya dace domin bada passport din ga 'yan kasarsu.
Sabon passport din dai zai shiga hannun mutanen Afirka ne a shekarar 2020, domin bada dama a gare su su shiga dukkanin kasashen mambobi ba tare da tarnaki ba.