An Kashe Wani Kusa Na Kungiyar al-qa'ida a arewacin Afirka
Jul 18, 2016 13:18 UTC
An Kashe Wani Kusa Na Kungiyar al-qa'ida a arewacin Afirka.
Kamfanin Dillancin Labarun "Associated Press" ya ambato kungiyar alqa'ida na sanar da mutuwar daya daga cikin kwamandojinta a arewacin Afirka.
Sanarwar ta kunshi cewa "Abubakar al-shanqidy, ya mutu ne a wani hari da su ka kaiwa sansanin sojan Mali da ke kan iyaka da kasar Borkina Faso.
Sai dai bayanin bai ambaci lokacin da aka kai harin ba da kuma yadda kwamandan na alqa'ida ya mutu ba.
Sai dai majiyar sojan Mali a yankin Koro, ta ce a ranar 10 ga watan Yuni ne wasu mutane da ba a san su ba sun kai hari wanda ya yi sanadin mutuwar sojojin Mali biyu.
Tags