Kungiyar Tarayyar Afrika Ta Sanar Da Shirin Janye Dakarunta Daga Kasar Somaliya
(last modified Tue, 19 Jul 2016 05:10:32 GMT )
Jul 19, 2016 05:10 UTC
  • Kungiyar Tarayyar Afrika Ta Sanar Da Shirin Janye Dakarunta Daga Kasar Somaliya

Kungiyar Tarayyar Afrika ta AU ta sanar da shirin fara janye dakarunta da suke aikin wanzar da zaman lafiya da sulhu a kasar Somaliya a shekara ta 2018.

A sanarwar da ya gabatar a yayin zaman kungiyar tarayyar Afrika a birnin Kigali fadar mulkin kasar Runwanda a jiya Litinin: Shugaban kwamitin kula da tsaro da sulhu na kungiyar tarayyar Afrika Isma'il Chergui ya bayyana cewa: Kungiyar Tarayyar Afrika zata fara janye dakarunta da suke aikin wanzar da zaman lafiya da sulhu a Somaliya {AMISOM} da nufin bai wa mahukuntan kasar damar fara jagorantar harkokin tsaron kasar ta Somaliya.

Isma'il Chergui ya kara da cewa: Za a fara aiwatar da shirin janye dakarun na {AMISON} ne daga farkon shekara ta 2018, kuma kafin wannan lokaci kwararru a harkar tsaro na kungiyar tarayyar Afrika zasu horas da jami'an sojin Somaliya tare da koyar da su dabarun yaki da ta'addanci.