Sojojin Somaliya Sun samu Nasarar Kwace Garin Qoryoley Daga 'Yan Ta'adda
Rundunar sojin gwamnatin Somaliya da hadin gwiwar dakarun wanzar da zaman lafiya da sulhu na kungiyar tarayyar Afrika sun samu nasarar kwace garin Qoryoley da ke kudancin kasar Somaliya daga mamayar mayakan kungiyar Al-Shabab.
Shugaban rundunar 'yan sanda a garin Qoryoley Ali Hasan ya sanar da cewa; Sojojin gwamnatin Somaliya da hadin gwiwar dakarun wanzar da zaman lafiya da sulhu na kungiyar tarayyar Afrika sun samu nasarar sake kwato garin Qoryoley daga mamayar mayakan kungiyar ta'addanci ta Al-Shabab a jiya Litinin.
Ali Hasan ya bayyana cewa: Tun a cikin daren Lahadi wayewar garin Litinin ne gungun 'yan ta'addan kungiyar Al-Shabab suka yi dirar mikiya kan garin na Qoryoley tare da kwace muhimman wajaje a garin musamman ofisoshin 'yan sanda, sansanonin soji, manyan ma'aikatun gwamnati da sauransu, tare da firgita jama'ar gari ta hanyar harbe-harbe.
Ya zuwa yanzu haka dai babu cikakken labarin irin hasarar da gumurzu a garin na Qoryoley ya haifar, sai dai bayan yin galaba a kan 'yan kungiyar ta Al-Shabab sun dauki matakin janyewa daga garin.