Karshen Taron (AU) Karo Na 27 A Kigali
-
Shugabannin kasashen Afrika a sahun gaba a taron (AU) karo na 27 a Kigali
A Jiya ne aka kammala taron shugabannin kasashe mambobin kungiyar tarayya Afrika karo na 27 a Kigali babban birnin kasar Rwanda.
Saidai a karshen taron Shugabannin sun gagara zabar sabon shugaban da zai gaji Mme Nkosazana Dlamini-Zuma domin jagorantar kungiyar.
Shugabannin dai sun kasa fahimtar juna akan sunayen 'yan takara dake neman shugabancin kungiyar, lamarin da ya sa aka jinkirta zaben har zuwa zamen kungiyar a watan Janairu mai zuwa.
Babu dai dan takara daya daga cikin ukun da suka hada da ministocin harkokin wajen Botswana da na Equatorial Guinea da kuma mataimakiyar shugaban kasar uganda daya samu adadin kuri'un da ake bukata.
Sama da shugabanni kasashe 20 sunyi rawa kuri'arsu, kuma galibinsu hujjar da suka bayar ita ce ta rashin tantancar 'yan takara.
Yanzu dai ya rage ga shugabannin su bukaci ga Dlamini Zuma ta tsawaita wa'adin jagorancinta ko kuma ta nada shugaba na rikon kwarya.
Dama kafin taron shugabanni kasashe 15 na yammacin nahiyar sun fitar da wata sanarwa ta bay daya inda suka bukaci dage zaben.
Enkhosazana Dlamini-Zuma, 'yar asalin kasar Afrika ta Kudu mace ta farko data shugabanci wannan kungiyar tun bayan kafa ta a cikin shekara 2002, lokacin da ta canza suna zuwa tarrayya Afrika.
ko baya ga gagarar zaben sabin shugaban kungiyyar, taron ya tattauna batutuwa da dama da suka hada da fitar da wani tsari na samar da zamen lafiya a kasar Sudan ta kudu da batun kirkiro da wani tsari na karbar kudin haraji domin tallafawa kungiyar.
Hakazalika kuma akwai bukatar neman dawowa daga cikin kungiyar daga kasar Maroko bayan ficewa na tsawan shekaru 30, da kuma samar da fasfo na bay daya na kasashen nahiyar ta Afrika.
A hannu daya kuma shugaban karba-karba na kungiyar kana shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya gabatar da shawara kafa wani asusu na nahiyar ta Afrika da za'a iya amfani dashi wajen ayyukan yaki da ta'adanci.
Haka kuma ya yi fatan ganin an kafa wata rundina Nahiyar ta kai dauki cikin gaggawa.