An kafa Kwamitin bincike kan kisan fararen hula a Somaliya
An kaddamar da Kwamitin bincike kan kisan fararen hula a Somaliya
Dakarun tsaro da sulhu na kasashen Afirka dake somaliya sun sanar a wannan Talata cewa sun kadamar da wani kwamitin bincike kan kisan da aka yiwa wasu fararen hula akalla 14 a wani kauye yayin gumurzu tsakanin Sojojinsu na mayakan kungiyar Ashabab.
sanarwar ta ce tun daga jiya Litinin Kwamitin ya fara gudanar da aikinsa kuma ana tsamani cikin kakkanan lokaci zai kamala aikinsa ya kuma gabatar da rahoto.
a ranar Lahadin da ta gabata ce wasu Sojojin Dakarun kungiyar Afirkan da ake kira da Amison kalkashin jagorancin Komandar Ethiopia, a yayin gumurzun da mayakan kungiyar Ashabab a kauyen Badawa suka cinnawa gidajen fula wuta lamarin da ya yi sanadiya akalla 14 daga mazauna kauyen.
Sanarwar farko da ta fito da Dakarun Afirkan, sun bayyana wannan hari a matsayin kuskure saidai tuni suka fara shan suka daga kungiyoyin kare hakin bil-adama da dama, lamarin da ya sanya suka kafa wannan kwamiti na gudanar da binciken.
Tun daga shekarar 2007 ne aka Tura Dakarun tsaro da sulhu na kasashen Afirka da yawan su ya kai dubu 22 a Somaliyan, Dakarun dai sun hada da Sojojin kasashen Kenya, Ethiopia, Burundi, Djibouti,da Uganda.