Zanga-zangar neman Sakin Shekh Ibarahim Azakzaky A Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8365-zanga_zangar_neman_sakin_shekh_ibarahim_azakzaky_a_najeriya
Kungiyar Matasa ta Abulfadl Abbas ta gudanar da zanga-zangar neman sakin shekh Ibrahim Alzakzaky a yankuna daban daban na kasar
(last modified 2018-08-22T06:58:37+00:00 )
Jul 19, 2016 12:58 UTC
  • Zanga-zangar neman Sakin Shekh Ibarahim Azakzaky A Najeriya

Kungiyar Matasa ta Abulfadl Abbas ta gudanar da zanga-zangar neman sakin shekh Ibrahim Alzakzaky a yankuna daban daban na kasar

Rahotanni dake fitowa daga Tarayyar Najeriya sun tabbatar da cewa a yau Talata matasan Kungiyar Abu Fadl Abas sun gudanar da zanga- zangar neman sakin Jagoran 'yan musulmi shekah Ibrahim Alzakzaky tare da mai dakinsa Malama Zinatudin Ibrahim a yankuna daban daban na cikin kasar

A Garin Gombe Zanga-zangar ta fara ne daga Anguwar Bulari inda aka bi ta gaban Majalisar jihar sannan aka kamala a gaban babbar kasuwar Jihar, mahalarta zanga-zangar na dauke da kyalaye gami da kwalaye da aka rubuta a sako  mana Jagoranmu, da kuma dariruwan 'yan uwanmu dake tsare a gidan Yari,dole a saki Shekh Zakzaky ba ma kaunar milkin danniya da zalinci.har ila yau mahalarta zanga-zangar na rera taken la'anta ga Haramcecciyar kasar Isla'ila.

A ranar 12 ga watan Satumbar shekarar da gabata ce Sojojin Najeriya suka buda wuta a kan 'yan uwa musulmi mabiya mazhabar shi'a almajiran shekh Ibarahim Alzakzaky a Garin Zariya a kan da'awar cewa sun tsarewa Babban kwamandan sojin kasa hanya kuma sun yi yukurin  kashe sa, inda suka kashe mutane da dama tare kuma da rusa gidan Shekh Ibrahim Elzakzaky da kuma Husainiyar Bakiyatul.., a cewar  Gwamnatin Jihar Kaduna Sojojin sun bisne Mutane sama da 347 daga cikin wadanda suka kashen a rami guda.