An Kafa Kotun Soji Don Hukunta Wasu Sojoji Uku Kan Rikicin Jos
Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da kafa wata kotun sojin da za ta yi shari'a wa wasu sojoji uku saboda rawar da suka taka yayin rikicin garin Jos na jihar Filato a Nijeriyan din wanda ya saba wa dokokin aikinsu.
Yayin da yake sanar da kafa kotun a barikin Rukuba da ke garin na Jos, Kwamandan rundunar tabbatar da zaman lafiya na musamman kan rikicin na Jos Manho Janar Tagbo Ude yace laifuffukan da ake zargin sojoji ukun sun tabka sun hada har da kisan gillan, lalata kayayyaki jama'a da na gwamnati kuma da kari kuma da ayyukan da suka saba wa irin ayyukan su na soji wanda ya saba wa dokokin sojin.
A bangare guda kuma Janar din ya tabbatar wa wadanda ake zargin da cewa za a yi musu shari'a bisa adalci ba tare da nuna wariya ba.
Jihar ta Filato dai ta fuskanci rikice-rikice na kabilanci da addini a lokuta da dama da suka yi sanadiyyar mutuwar wani adadi mai yawa na al'ummar jihar inda a lokuta da dama ake zargin jami'an tsaron Nijeriyan kama daga sojoji da 'yan sanda da cin zarafin mutane.