Najeriya : MSF Ta Kadu Kan Halin Da Ake Ciki A Borno
Kungiyar likitoci marar iyaka ta MSF ta nuna matukar damuwa kan halin da 'yan gudun hijira ke ciki a Borno saboda matsallar boko Haram da yankin ya yi fama dashi.
Bayan wani ran gadi na tsawan kwana goma a yankin da tawagar likitocin ta kai, kungiyar ta MSF ta ce jama'a na cikin masifa musamen a yankin Bama dake nisan kilomita 70 daga Maiduguri babban birnin jihar Borno.
A wani taron manemai a Paris, darectar kula da ayyukan kungiyar ta MSF, Dr Isabelle Defourny ta ce lamarin na bukatar agaji cikin gaggawa.
Kimanin mutane 10,000 ne ke gudun hijira a yankin kuma dubbai daga cikin su na fama da matsananciyyar matsalar karamcin abunci.
Wasu alkaluma da kungiyar ta fitar sun nuna cewa kashi 19% na yara kanana 804 data yi wa bincike lafiya ya nuna cewa suna fama da matsananciyyar matsalar karamcin abunci.
A sansanin Bama kawai kiyatsin ya nuna cewa kimanin mutane 200 ne suka rasa rayukan su daga ranakun 23 na watan Mayu zuwa 20 ga watan Yuni na wannan shekara.