Dubban 'Yan Sudan Ta Kudu Sun Gudu Zuwa Kasar Uganda
Majalisar Dinkin Duniya Ta ce Dubban 'Yan kasar Sudan ta Kudu Sun Gudu Zuwa Kasar Uganda.
Majalisar Dinkin Duniya Ta ce Dubban 'Yan kasar Sudan ta Kudu Sun Gudu Zuwa Kasar Uganda.
Kamfanin Dillancin Labarun Xinhua ya ambato hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya, na cewa; Fiye da mutane dubu 10 ne su ka gudu daga Sudan ta kudu zuwa kasar Uganda a cikin kwanaki biyu da su ka gabata.
Rahoton ya ci gaba da cewa; A ranar talatar da ta gabata kadai mutane dubu 7 su ka bar kasar, yayin da wasu karin dubu 3 su ka fice a ranar larabar da ta gabata.
Wani sashen na rahoton ya kara da cewa, mafi yawancin wadanda su ke isa kasar ta Uganda, suna fama da yunwa ko rashin abinci mai gina jiki.
A ranar 7 ga watan Yuli ne dai fada ya barke a tsakanin magoya bayan shugaban kasar Sudan ta kudu Silva Kiir da kuma mataimakinsa Reik Machar.