Turkiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8479-turkiya
Tarayyar Turai Ta Bukaci Turkiya Da Ta yi Aiki Da Doka
(last modified 2018-08-22T11:28:38+00:00 )
Jul 22, 2016 06:34 UTC
  • Turkiya

Tarayyar Turai Ta Bukaci Turkiya Da Ta yi Aiki Da Doka

Jami'ar harkokin Waje ta tarayyar turai Fedrica Mogherini ta soki gwamnatin  kasar Turkiya saboda take doka da kuma takura 'yan hamayya.

A wani bayani na da jami'ar harkokin wajen ta turai ta fitar a jiya alhamis,  ta bukaci kasar Turkiya da ta yi aiki da doka da oda,  ta kuma girmama hakkin bil'adama.

Har ila ya Mogherini ta yi suka akan yadda gwamnati ta ke fakewa da batun juyin mulki domin takuwara abokan hamayya.

A jiya alhamis ne dai majalisar dokokin kasar ta amince da kafa dokar ta baci a cikin kasar.