Ziyarar Manzon China zuwa kasar Sudan ta Kudu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8485-ziyarar_manzon_china_zuwa_kasar_sudan_ta_kudu
Wakilin kasar China a harakokin yankin Afirka ya kai ziyara kasar Sudan ta Kudu
(last modified 2018-08-22T06:58:38+00:00 )
Jul 22, 2016 04:03 UTC
  • Ziyarar Manzon China zuwa kasar Sudan ta Kudu

Wakilin kasar China a harakokin yankin Afirka ya kai ziyara kasar Sudan ta Kudu

Mista Jank Jian hawa ya kai ziyarar ne domin tattaunawa da magabatan kasar a kan halin da kasar  ke ciki, bayan kasar ta sudan ta kudu ana sa ran wakilin na china zai kai ziyara kasashen Uganda, Ethiopia da kuma Kenya domin tattaunawa da magabatan kasar a kan halin da Sudan ta kudun ke ciki.

Wannan ziyara ta Mista Jank Jin na cewa ne a yayin da wasu mahara suka kaiwa Dakarun tsaro da sulhu na MDD hari a kasar Sudan ta kudun, inda suka hallaka Sojojin China biyu, bayan wannan hari, a ranar Litinin din da ta gabata, China ta fara kwashe Jami'an Diplomasiyarta daga kasar Sudan ta kudun.

A wata sanarwa da Kakakin Ma'aikatar harakokin wajen China ya fitar a wannan Alkhamis,ya ce  duk da cewa an dakatar da buda wuta a Sudan ta kudun, amma har yanzu kasar na cikin mawuyacin hali, domin haka wajibi ne su tattauna da magabatan kasar

Kasar China dai nada Sojoji dubu biyu da 700 dake aikin tabbatar da tsaro da sulhu a yankin Afirka, daga cikin wannan adadi, an kashe Sojojin nata guda 13.